Yanzu haka, ana tsare shi a wani gidan yari da ke birnin Tripoli, kuma gwamnatin wucin gadin kasar za ta yanke masa hukunci.
Tuni dai a wannan rana, gwamnatin Tunisiya ta ba da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, an mika Mahmoudi zuwa ga hukumar Libya, amma daga bisani kuma, kakakin fadar shugaban kasar Tunisiya ya ba da sanarwa cewa, shugaban kasar Tunisiya bai daddale ko wace yarjejeniya ba da ke shafar tusa keyar Mahmoudi zuwa Libya, kuma ba ya da masaniya game da mika Mahmoudi zuwa hukumar Libya, idan aka tabbatar da wannan labari, to, fadar firaministan kasar za ta dauki nauyin tusa keyar shi zuwa Libya.
A watan Satumba na shekarar 2011 ne, aka tsare tsohon firaministan kasar Libya Mahmoudi a kasar Tunisiya sakamakon shiga kasar ta barauniyar hanya, kuma kotun binciken laifuffuka ta kasar ta yanke masa hukuncin dauri har na watanni 6, sa'an nan kuma, aka ci gaba da tsare shi a kasar ta Tunisiya.(Bako)