Bisa labarin da aka samu, an ce, Mohammed Maqrif ya kama aikin shugaban majalisar dokokin jama'ar kasar Libya a watan Agusta na shekarar 2012, kuma yana daya daga cikin shugabanni masu lura da harkokin mulkin kasar a halin yanzu.
Wannan shi ne karo na biyu da Mr. Mohammed Maqrif ya ci nasarar tsallake rijiya da baya daga harin da aka kai masa. An taba kai masa hari a watan Janairu na shekarar 2013 yayin da yake wani otel a garin Sebha da ke kudancin Libya, inda wasu dakarun da ba a tabbatar da asalinsu ba suka harba bindigogi a otel din. A sanadiyar wannan hari, masu gadi guda uku sun jikkata, amma Mohammed Maqrif bai ji rauni ko kadan ba. (Maryam)