in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Libya ta mamaye yammacin yankuna na manyan gurabai 2 da sojojin Muammar Gaddafi suka mallaka
2011-10-18 18:45:32 cri

A ran 17 ga wata, kakakin sojojin gwamnatin kasar Libya Ahmed Omar Bani ya bayyana cewa, a kwana baya, sojojin gwamnatin sun mamaye yammacin yankuna na manyan birane 2 da masu nuna goyon baya ga Muammar Gaddafi suka mallaka, yanzu, suna kokarin kame sauran sojojin Muammar Gaddafi.

A wannan rana, a birnin Tripoli, Ahmed Omar Bani ya bayyana cewa, yawan yankunan birnin Bani Walid da sojojin gwamnatin kasar suka kamne ya kai kashi 90 cikin kashi 100, za su iya mamaye birnin cikin sauri.

Game da halin da ake ciki a birnin Sirte, Ahmed Omar Bani ya bayyana cewa, yanzu, masu nuna goyon baya ga Muammar Gaddafi suna jibge a cibiyar birnin, a ganin sojojin gwamnatin kasar, mai yiyuwa ne wasu jami'ai mutane na gwamnatin Muammar Gaddafi suna zaune a wannan wuri.

A wannan rana, ministan tsaro na kasar Amurka Leon Panetta ya bayyana cewa, yanzu, magoya bayan Muammar Gaddafi suna yin yaki a birnin Sirte, don haka, sojojin kasashen Turai ba za su daina harin da suke kai wa kasar Libya ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China