A lokacin ziyarar da suka yi, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, babban burin ziyararsa shi ne sake nuna cewar M.D.D ta nuna goyon baya ga jama'ar kasar Libya da suke neman samu 'yancin kai da dimukuradiyya, da sa kaimi ga gwamnatin wucin gadi ta kasar Libya da ta yi kokari wajen samu ra'ayi daya tare da bangarori daban daban, yin hadin kai, kiyaye zaman lafiya da sa kaimi ga jintuwar al'ummar kasar.
Wannan ziyara shi ne karo na farko da Ban Ki-Moon ya kai kasar Libya bayan da aka hambarar da gwamnatin Gaddafi. Yanzu, wannan tawagar musamman da ta nuna goyon baya ta ga Libya ta M.D.D za ta ba da taimako ga kasar wajen sake gina ta da share fage ga babban zaben kasar.
A sa'i daya kuma, ko da yake kungiyar NATO ta kammala aikin soja a kasar Libya, amma, a ran 2 ga wata, ma'aikatan harkokin waje ta kasar Rasha ta gabatar da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, kasar tana da wasu shakku game da aikin soja da kungiyar NATO ta kai kasar Libya, kuma ya kamata bangarorin da abin ya shafa su yi nazari kan wannan aikin soja, don amfani da darasin da wannan aikin soja ya kofar.(Abubakar)