in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya tana maraba da masana'antun Sin da su sake komawa kasar
2011-12-23 16:40:28 cri

A ranar 22 ga wata, ministan harkokin waje na gwamnatin wucin gadi na kasar Libya Ashour Ben Khayil ya bayyana cewa, yanzu, gwamnatin wucin gadi na binciken yarjejeniyoyin gine-gine da aka daddale tsakanin Libya da kamfanoni na sauran kasashen duniya, yana fatan kamfanonin kasar Sin za su gaggauta komawa kasar Libya don shiga aikin sake gina kasar, kana, ya yi maraba da masana'antun Sin da su gaggauta komawa kasar.

A wannan rana, a birnin Tripoli babban birnin kasar, yayin da Minista Khayil ke ganawa da jakadan Sin da ke kasar Libya Wang Wangsheng, ya bayyana cewa, gwamnatin Libya ta dora muhimmanci sosai game da rawar da Sin ke takawa wajen daidaita manyan batutuwan duniya, yana fatan inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da mu'amalar siyasa da kasar Sin, da kara fahimtar juna, kana kuma ya ce, gwamnatin wucin gadi tana fatan taimakawa kamfanonin Sin da kawo musu sauki.

A nasa bangare kuma, Wang Wangsheng ya ce, kasar Sin za ta sa himma wajen sake gina kasar Libya bayan yake-yake, kuma tana fatan shiga cikin wannan aiki.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China