A kauyen Yilite dake birnin Ulanhot, na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin, akwai wani wurin musamman da aka yiwa lakabi da “Daular Dawisu”, wanda ba aljanna ce kadai ga dawisu ba, har ma wata sabuwar duniya ce ga mazauna kauyen, domin suna kara samun kudin shiga da wadata. Wadda ta kirkiro wannan duka ita ce Zhou Haiyan, wadda aka fi sani da “Sarauniyar Dawisu”. Mace ce da ta yi amfani da hazaka, don mayar da aikin kiwon dawisu a matsayin wata hanyar samun wadata ga mazauna kauyen na Yilite.
Kwanan ne shahararren matashin darektan shirya fina-finai daga Jamhuriyar Nijar malam Laouali Gazali, ya jagoranci wata tawagar daukar fim zuwa kasar Sin, musamman birnin Beijing, da jihar Xinjiang, don gudanar da ayyukan daukar fina-finai bisa hadin-gwiwa da sashin Hausa na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice. Kafin kammala ayyukansu a kasar Sin, Murtala Zhang ya samu damar zantawa da Laouali Gazali ta waya, inda ya yi karin haske game da abubuwan da suka burge shi a wurare daban-daban na kasar Sin...
Noma na daya daga cikin mafi dadewa kuma mafi muhimmanci aiki na dan Adam, domin tana samar da kayan masarufi na rayuwa da walwala. Kuma noma na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki, Noma na tallafawa ci gaban zamantakewar al'umma ta hanyar inganta rayuwa, ilimi da lafiyar al'ummomin karkara. Har ila yau noma na samar da hadin kan jama'a, da daidaita bambancin al'adu da daidaiton jinsi. Noma na iya rage kaura zuwa birane, da rage yunwa da rashin abinci mai gina jiki, da karfafa mata da matasa.
Cikin tsawon sa’o’i 2 da mintuna 7, matashi Li Zezhou dan shekaru 17 a duniya, wanda ke da matsayi na 2 na larurar gani, ya kammala tseren da ya gudana ranar Lahadin karshen makon jiya, a gasar tseren fanfalaki ko “Marathon” ta shekarar 2024 da aka yi a birnin Tianjin. Matashi Li ya kammala tseren rabin zango na Marathon a karon farko na shigarsa irin wannan gasa.
A ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin ta dage kan cewar, dukkan kabilun kasar daidai suke da juna. Kana ana kokarin neman sanya al'ummar kasar Sin zama wata al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, wadda ta fi samun goyon baya daga al'ummun kasar, da cikakkiyar damar tabbatar da hadin kansu. A cikin shirin Allah Daya Gari Bamban na yau, za mu duba yadda Sinawa ke kokarin tabbatar da hakan.