2020-07-31 11:33:04 cri |
A shekarar 1994 ne, aka fara gina tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3. Cikin shekaru 26 da suka gabata, gaba daya, kasar Sin ta gudanar da ayyukan harba tauraron dan-Adam sau 44. Kuma, bi da bi, ta harba taurarin dan-Adam na BeiDou-1 guda hudu, da taurarin dan-Adam na BeiDou-2 guda 55 da tauraron dan-Adam na BeiDou-3 kuma duk sun shiga hanyoyin da aka tsara, ta hanyar yin amfani da rokar harba tauraron dan Adam samfurin ChangZheng-3. A bana, an kammala tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 bisa dukkanin fannoni, wanda zai ba da hidima ga al'umomin duniya a fannin sanin inda suke.
Kasar Sin ce dai, ta kera dukkan muhimman sassan tauraron dan-Adam na BeiDou-3. Yanzu haka, akwai kasashe 137 da suka kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwar tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3.
Shi dai wannan tsarin tauraron dan-Adam na BeiDou, yana daya daga cikin tsare-tsaren shawagin taurarin dan-Adam guda hudu dake aiki a duniya, da suka hada da GPS na Amurka, da GLONASS na kasar Rasha, sai kuma Galileo na kungiyar tarayyar Turai. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China