Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na shirin harba taurarin dan Adam biyu zuwa duniyar Mars
2020-07-21 10:04:53        cri

Yanzu haka an kammala yiwa wasu taurarin dan Adam biyu sauye sauye, kafin harba su zuwa duniyar Mars, karkashin shirin da aka yiwa lakabi da Tianwen-1.

Taurarin biyu, wato Tianlian I-02 da Tianlian II-01, za su yi aiki musayar bayanai ne masu nasaba da zirga zirga, da lura da na'urorin binciken duniyar ta Mars dake kan falakin su.

Tun a ranar 17 ga watan nan ne dai aka kai rokar Long March-5 ta hudu, wadda za a yi amfani da ita wajen harba taurarin biyu zuwa Mars, a tashar Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar ta Sin.

Ana fatan harba rokar ta March-5 Y4, nan gaba a karshen watan nan na Yuli, ko kuma farkon watan Agusta dake tafe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China