Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta harba sabon tauraron dan Adam mai samar da hotunan duniyar bil Adama
2019-11-28 17:09:13        cri

Sin ta harba sabon tauraron dan Adama na hangen duniyar bil Adama, ta amfani da rokar Long March-4C, daga tashar harba taurarin dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an harba sabon tauraron mai lakabin Gaofen-12 ne da karfe 8 saura mintuna 8 na safiyar yau Alhamis din nan, bisa agogon birnin Beijing. Masu aikin harba tauraron sun ce tuni ya shiga falakin sa cikin nasara.

Harba wannan sabon tauraro dai daya ne daga matakan aiwatar da shirin kasar Sin, na sanya ido da nazarin duniyar bil Adama daga sararin samaniya, bisa fasahohi masu karfin samar da managarcin sakamako ta hotuna masu inganci.

Za a ci gaba da aiki da tauraron Gaofen-12, wajen ayyukan safiyon doron kasa, da tsara taswirar tituna, da kiyasta yabanya, tare da tallafawa ayyukan ba da taimako yayin aukuwar annoba. Har ila yau, tauraron zai taimakawa ayyukan da ake gudanarwa karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China