Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta yi kokarin cika alkawarun da ta yiwa 'yan uwanta kasashen Afirka
2019-12-24 19:19:56        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya bayyana cewa, tauraron dan-Adam din kasar Habasha da kasar Sin ta harba mata, zai taimakawa kasar wajen gudanar da bincike game da matsalar sauyin yanayi da sauran fannoni, zai kuma bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar kasar.

Wannan na zuwa ne, bayan taurarin dan-Adam na kasashen Najeriya da Aljeriya da sauran kasashe da kasar Sin ta taimaka wajen harbawa. Ya ce, Kasar Sin za ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin ta cika alkawarun da ta yiwa 'yan uwanta kasashen Afirka.

Geng ya jaddada cewa, masana daga kasashen Sin da Habasha sun dade suna aiki tare don raya fannin tauraron dan-Adam, haka kuma kasar Sin ta horas da ma'aikatan da za su kula da tauraron dan-Adam din kasar da ma sauran fannoni.

Bayan tauraron dan-Adam din ya shiga falaki, kasar Habasha za ta rika sarrafa wa da ma yin amfani da shi da kanta.

Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, kasashen Sin da Afirka sun kasance tamkar al'umma mai makomar bai daya kana al'umma mai muradun alakar moriyar juna. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da kasashen Afirka don bunkasa hadin gwiwa a fannoni da dama da suka hada da hadin gwiwar sararin samaniya, da taimakawa 'yan uwanmu kasashen Afirka, ta yadda za su cimma burinsu ba tare da bata lokaci ba bisa matsayi mai inganci da cimma nasarar alakar moriyar juna da bunkasuwa tare tsakanin Sin da Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China