Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta shirya harbar taurarin dan Adam na Beidou a watannin Maris da Mayun bana
2020-02-24 12:21:45        cri

Rahotanni daga ofishin kula da tsarin tauraron dan-Adam na kasar Sin na nuna cewa, kasar Sin ta shirya harba taurarin dan Adam na Beidou a watannin Maris da Mayun bana, wanda zai kasance karo na karshe, ta yadda za a kammala kafa tsarin zirga-zirgar taurarin dan Adam na Beidou a duk fadin duniya.

A ranar 14 ga watan Febrairun bana, rokar Changzheng-3 ta isa filin harbar tauraron dan Adam na Xichang kamar yadda aka tsara, wanda a karon farko a bana, zai yi dakon tauraron dan Adam na Beidou zuwa saurarin samaniya. Yanzu ana gudanar da mabambantan ayyukan gwaji kan rokar da kuma taurarin dan Adam na Beidou da suka isa filin.

A ranar 15 ga wata kuma, an kammala gwajin yadda tauraron dan Adam na Beidou na 41, 49, 50, 51 zai shiga falaki, ta yadda wadannan taurarin dan Adam 3 za su fara ayyukansu na zirga-zirga a hukumance, hakan zai ci gaba da kyautata tsarin Beidou na nuna hanyoyi ba tare da wata matsala ba.

Bayan da aka harba taurarin dan Adam na Beidou a watannin Maris da Mayun bana, kasar Sin za ta cimma burin kasar ta a fannin tsarin tauraron dan-Adam a fadin duniya, wanda ta shafe shekaru da dama tana kokarin cimmawa. Yanzu dukkan sassa masu ruwa da tsaki suna gaggauta share fagen, a kokarin tabbatar da samun nasarar kammala aikin kamar yadda aka tsara.(Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China