2020-04-01 10:31:15 cri |
Ta hanyar amfani da hadakar fasahohin samar da hidima na kai tsaye, injunan na iya zuba taki daidai-wa-daida gwargwadon bukata.
A cewar Zhang Ruihong, farfesa a jami'ar Yangzhou kuma shugaban tawagar da ta kera injunan zuba takin, yayin da tafiyar inji ya kauce hanya, tsarin tauraron zai daidaita shi a daidai lokacin.
Han Baolong, manomi a wani kauye, ya ce injin raba takin mai sarrafa kansa, ya taimaka masa sosai, saboda bayan barkewar kwayar cutar Corona a watan Junairu, an yi rashin ma'aikata masu zuba taki da magungunan kashe kwari. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China