Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta harba karin taurarin dan Adam na binciken kimiyya
2020-01-27 16:10:39        cri
Cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin CAS, ta ce nan da shekaru 3 zuwa 4, kasar za ta harba karin taurarin dan Adam na binciken kimiyya, wadanda za a yi amfani da su wajen gano maganadisun lantarki ko "electromagnetic signals" masu nasaba da motsin maganadisu, da sauyawar yanayin rana, da bincike kan falakin duniyoyi, da cudanyar iska mai nasaba da rana da kuma maganadisun duniya.

Kafin hakan, CAS ta yi nasarar harba makamantan wadannan taurarin da dama, ciki hadda mai lakabin "Dark Matter Particle Explorer", da Taiji-1, wanda shi ne tauraron dan Adam na farko mallakar kasar Sin, wanda ya gudanar da binciken kimiyya da dama masu alaka da tasirin maganadisun sararin samaniya, da gano wanzuwar igiyoyin maganadisu.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China