Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam don sanya ido kan teku
2020-06-11 09:04:18        cri

Kasar Sin ta cimma nasarar harba tauraron dan Adam mai lakabin HY-1D ta amfani da rokar Long March-2C, tauraron da zai taimaka wajen ayyukan sanya ido a teku.

An dai harba tauraron ne daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Taiyuan dake lardin Shanxi, da karfe 2:31 na safiyar yau Alhamis bisa agogon birnin Beijing.

A cewar hukumar lura da harkokin sararin samaniyar kasar Sin, sabon tauraron zai kasance na farko cikin rukunin makamantansa, wanda za a yi amfani da su wajen ayyukan da ba na soji ba a teku, tare da wani tauraron mai lakabin HY-1C, wanda aka harba tun cikin watan Satumbar shekarar 2018.

Harba tauraron na yau, shi ne karo na 33 da aka yi amfani da nau'in rokar Long March wajen gudanar da irin wannan aiki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China