Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran Amurka: Kamfanonin ketare ba su son yanke dangantaka tsakaninsu da tattalin arzikin Sin
2020-06-16 14:20:57        cri

Jiya Litinin, jaridar The New York Times ta fidda wani sharhi mai taken "ko kuna son yanke dangantakar dake tsakaninku da tattalin arzikin Sin? Masana'antu a fannoni uku ba za su yarda ba".

Cikin sharhin, an bayyana cewa, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya zama fatanmu na karshe, wajen dakile raguwar tattalin arzikin duniya, kuma kamfanonin ketare ba su son yanke dangantakar dake tsakaninsu da tattalin arzikin kasar Sin.

Daga shekarar 2000, kasar Australia ta fara sayar da galibin amfanin ruwa na lobster na kasar a kasar Sin. Ya zuwa farkon bana, kasar ta sayar da lobster nata da yawan su ya kai kaso 95 bisa dari a kasar Sin. Amma yanzu kasar Sin ta dakatar da sayan lobster daga kasar, sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19.

Kuma ko da yake wasu sun yi kira ga kasar Australia da ta dogara kan kasuwar kanta, amma Australia ba ta taba janye jiki daga kasuwannin kasar Sin ba. A halin yanzu, tana samar da manufofin rangwame domin dawowa kasuwannin kasar Sin.

Mai jagorar kamfanin samar da fitilu na Osram, wanda hedkwatarsa a birnin Munich na kasar Jamus take, Olaf Berlien ya bayyana cewa, babu kasuwanni a sauran kasashen duniya da za su iya maye gurben kasuwannin kasar Sin, ta fuskar raya tattalin arzikin duniya baki daya.

Kamfanin Toto shi ne kamfanin kera masai mafi girma a kasar Japan. A bara, ya sayar da rabin kayayyakinsa zuwa kasar Sin, ya kuma kafa kamfanoni guda 7 a kasar Sin. A watan Janairu da watan Fabrairu na bana, kamfanin Toto ya daina samar da kayayyaki a masana'antunsa, sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya haddasa hasara gare ta, amma duk da haka, bai taba zaton janye jiki daga kasuwannin kasar Sin ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China