Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta jaddada bukatar cimma muradun ci gaban tattalin arziki da zaman takewa na 2020
2020-05-30 15:52:58        cri
Taron majalisar zartarwar kasar Sin da aka yi a jiya Juma'a, ya jaddada batun aiwatar da dabaru da ayyukan da za su kai ga cimma muradun kasar na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na 2020.

Taron wanda ya gudana karkashin firaministan kasar Li Keqiang, ya ce rahoton ayyukan gwamnati da aka amince da shi lokacin kammala taro na 3 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 13, ya tsayar da muradun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa da muhimman ayyuka da ake son cimmawa a bana, yana mai bukatar gwamnatoci a dukkan matakai su aiwatar da dukkanin ayyukan tare da kammala su.

An kuma samar da wata dabara ta musamman da nufin tabbatar da kudade sun tafi kai tsaye zuwa matakan karkara da kuma amfani da su yadda ya kamata. Ya kara da bayyana cewa, kamata ya yi dukkanin bangarorin kasuwanci, ciki har da kanana da matsakaitan kamfanoni tare da mutane masu bukata, su amfana daga dabarun.

A cewar taron, ya kamata samar da yanayin kasuwanci da zai karbu a duniya da biyan bukatun masu sayayya da kiyaye doka, tare da inganta takara bisa adalci, su zama muhimman abubuwa a cikin ajandar aikin gwamnati. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China