Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IMF ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin duniya na 2019
2019-10-16 10:47:17        cri
Asusun bada lamuni na duniya IMF, ya rage hasashen da ya yi na karuwar tattalin arzikin duniya a bana zuwa kaso 3.

Rahoton da asusun ya fitar jiya, kan hasahen tattalin arzikin duniya, ya ce ci gaban tattalin arzikin ya ragu da kaso 0.2 daga kiyasin da aka yi a watan Yuli.

Babbar masaniyar harkokin tattalin arziki ta asusun, Gita Gopinath, ta ce wannan ne karon farko da karuwar tattalin arzikin ke jan kafa sosai, tun bayan matsalar kudi da duniya ta shiga, inda ta ce karuwar shingen cinikayya da rikice-rikice a yankuna, na ci gaba da raunana ci gaban tattalin arzikin.

Ta kara da cewa, wasu batutuwa na cikin gida suke rage saurin ci gaba a kasashe masu tasowa, yayin da raguwar ci gaba a fannin gudanar da ayyuka da yawan tsoffi fiye da matasa ke daga cikin matsalolin kasashe masu ci gaba.

Rahoton ya kuma nuna cewa, manyan kasashe na ci gaba da jan kafa wajen kara karfinsu na neman samun ci gaba mai dogon zango, inda ci gaban na su ya sauka zuwa kaso 1.7, idan aka kwatanta da kaso 2.3 na shekarar 2018.

Haka zalika ci gaban kasashe masu tasowa, wanda ya ragu zuwa kaso 3.9 a bana, maimakon kaso 4.5 da ya kasance a bara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China