Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasa duk da takaddamar cinikayya da Amurka in ji wani kwararre
2019-07-22 13:21:50        cri

Wani masanin tattalin arziki dan kasar Jordan, ya ce tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka, duk kuwa da takaddamar cinikayyar dake wakana tsakanin kasar da Amurka.

Mr. Khaled Zubeidi ya ce Sin na da alaka mai karfi tsakaninta da Latin Amurka, da nahiyar Afirka, da Rasha, da Turai da Asiya, wanda hakan ke haifar da karsashi ga tattalin arzikin kasar duk kuwa da tasirin waccan takaddama.

Da ma dai tuni hukumar kididdiga ta kasar Sin, ta fitar da alkaluma dake nuna cewa, cikin watanni 6 na farkon shekarar bana, tattalin arzikin kasar ya karu da kaso 6.3 bisa dari, wanda adadinsa ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 45.09, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.56. Wannan ci gaba dai da aka samu a cewar hukumar, yana da alaka ne da kwazon gwamnati na daukar matakan cimma nasarar bunkasa tattalin arzikin kasar, da kaso 6 zuwa 6.5 bisa dari tsakanin wannan lokaci.

Masanin ya kara da cewa, tsarin tattalin arzikin Sin na bin wani salo ne, wanda ke ba shi damar jure matsin da takaddamar tattalin arzikin da Amurka ta tayar ke haifarwa, kuma ko shakka babu hakan zai cutar da bangaren Amurka.

A nasa tsokaci, shugaban cibiyar bunkasa cinikayya ta Amman Haj Tawfiq, cewa ya yi bunkasar tattalin arzikin Sin a watanni 6 na farkon wannan shekara, ya nuna cewa kasar na da zarafin kare kai daga tasirin takaddamar cinikayya. Ya ce shawarar Sin ta ziri daya da hanya daya ko BRI, ta haifar da sabon tsarin bunkasa tattalin arziki, da cudanyar sassa mabanbanta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China