Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi gargadin cewa takaddamar cinikayya za ta lahanta ci gaban tattalin arzikin duniya
2019-05-22 16:07:21        cri
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto kan hasashen yanayin ci gaban tattalin arzikin duniya a tsakiyar shekarar 2019, inda ta bayyana cewa, duba da tsanantar takaddamar cinikayya gami da rashin tabbas na manufofin kasa da kasa, karuwar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya.

Rahoton ya yi nuni da cewa, sakamakon dalilan da suka shafi gida da waje, an yi hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya zai ragu zuwa kaso 2.7 bisa dari a shekarar da muke ciki, wanda ya yi kasa da hasashen da aka yi a farkon bana, wato kaso 3 bisa dari. Haka kuma har yanzu an gaza daidaita tankiyar cinikayya yadda ya kamata, sai ma kara buga harajin kwastam. An rage hasashen da aka yi kan saurin karuwar cinikayyar duniya a bana zuwa kaso 2.7 bisa dari, wanda ya yi kasa da kaso 3.4 bisa dari na bara.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China