Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin na iya samun babban tagomashi in ji wani masani
2020-06-12 13:34:38        cri

Babban masanin tattalin arziki a bankin Deutsche Mr. Michael Spencer, ya ce tattalin arzikin kasar Sin na iya sake samun kyakkyawan inganci da ci gaba, bayan shawo kan cutar COVID-19.

Mr. Spencer ya ce, yayin da manyan kasashen duniya da dama ke kokarin sassauta matakan kulle da suke aiwatarwa don dakile yaduwar cutar, suke kuma samun sauki daga komadar tattalin arziki, a hannu guda Sin na cikin kasashe 'yan kalilan da ke iya samun bunkasuwa.

Masanin wanda ke jagorantar cibiyar binciken yanayin tattalin arziki ta Asiya da Pacific, ya kara da cewa, akwai alamu dake nuna cewa, farfadowar da Sin za ta yi, za ta bada sha'awa matuka, inda ake sa ran tattalin arzikinta zai bunkasa, da kaso 5 zuwa 6 bisa dari a watannin Afirilu da Yuni, bayan koma baya da ta fuskanta a watannin 4 da suka gabaci hakan. Kaza lika sashen bukatun hajoji a cikin kasar tuni shi ma ya farfado yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China