Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu raguwar koma bayan masana'antar samar da manhaja ta kasar Sin
2020-06-01 10:06:18        cri
Ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce an samu sauri a fannin farfadowar masana'antar samar da manhaja a kasar a watannin baya-bayan nan, inda riba da kudin shiga da yanayin daukar ma'aikata a masana'antar ya samu saurin ci gaba.

Alkaluman da aka fitar a baya-bayan nan sun nuna cewa, daga watan Junairu zuwa Afrilu, kamfanonin samar da manhaja sun samu kudin shigar da ya kai yuan triliyan 2.08, kwatankwacin dala 293, wanda ya yi kasa da kaso 0.1 akan na bara.

Ribar masana'antar ta sauka da kaso 2.3 zuwa yuan biliyan 239, idan aka kwatanta da raguwar kaso 13.1 da aka samu a rubu'i na farkon bana, abun da ya nuna cewa, sannu a hankali, ana samun farfadowar bangaren, wanda annobar COVID-19 ta yi wa mummunan tasiri.

Bisa la'akari da yadda annobar COVID-19 ke tasiri a wajen kasar Sin, fitar da manhaja zuwa ketare na samun jinkiri a dan tsakanin, wanda ya sauka da kaso 13.5 a kan na bara.

Cikin watanni 4 na farkon bana, masana'antar ta dauki mutane miliyan 6.59 aiki, adadin da ya karu da kaso 0.2 a kan na makamancin lokacin a shekarar da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China