Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta nuna matukar kwarin gwiwa cikin kasashe mafiya bunkasar tattalin arziki a shekarar 2020
2020-01-21 09:48:03        cri
Kasar Sin ta nuna matukar kwarin gwiwa tsakanin kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya, yayin da kashi 45 bisa 100 na manyan jami'an zartaswa wato CEOs suka bayyana cewa suna da matukar kwarin gwiwar bunkasuwar kudaden shiga a shekarar nan ta 2020, hakan na kushe ne cikin rahoton bincike na shekara na manyan jami'an zartaswar kamfanoni wato CEOs na duniya na kamfanin bin diddigi da ayyukan kwararru na kamfanin PwC.

Rahoton wanda aka kaddamar gabanin taron kolin tattaunawar tattalin arziki na kasa da kasa a Davos na kasar Switzerland ranar Litinin, binciken shi ne karo na 23, ya nuna cewa yawan CEOs masu cike da kwarin gwiwa na yiwuwar samun bunkasar tattalin arzikin duniya cikin watanni 12 ya kai kaso 36 bisa 100 a Amurka, kashi 27 a Canada, sai Jamus da kashi 20 bisa 100, yayin da kashi 11 bisa 100 kawai a Japan.

A cewar binciken, CEOs ba su da yakini game da hasashen kamfanoninsu a shekara mai zuwa, yayin da kashi 27 ne kadai na CEOs suke da cikakken kwarin gwiwa game da bunkasar kamfanoninsu a cikin watanni 12 masu zuwa, adadin da ya kai matsayin mafi kankanta tun bayan shekarar 2009, wanda ya yi kasa da kashi 35 bisa 100 a shekarar da ta gabata. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China