2019-12-19 10:54:02 cri |
A yayin ganawar tasu, Shao Hong ya ce, kasar Benin dadaddiyar abokiyar kasar Sin ce a yammacin nahiyar Afirka, kuma muhimmiyar abokiyar hadin gwiwar kasar Sin ce. kasar Sin tana son hada kai da kasar Benin wajen aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, domin samun sakamako mai gamsarwa da kuma tallafawa al'ummomin kasashen biyu.
A nasa jawabin, shugaba Talon ya nuna yabo matuka kan dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da kasarsa, ya kuma taya kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Haka kuma, ya ce, yana fatan karfafa mu'amalar dake tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban yadda ya kamata. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China