Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararru da masana dabaru sun bukaci a dauki matakan gaggawa game da illolin sauyin yanayi a Afrika
2019-12-11 10:24:55        cri
Wasu kwararrun kasashen Afrika da masu tsara manufofin cigaba sun bukaci shugabannin Afrika da cibiyoyin raya nahiyar da su dauki kwararan matakan gaggawa domin dakile mummunan tasirin da matsalar sauyin yanayi zai iya haifarwa nahiyar baki daya.

Sun yi wannan kira ne a ranar Talata a lokacin taron shekara shekara na wakilan dindindin na kungiyar tarayyar Afrika (AU), gami da wakilan hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), taron wanda ya mayar da hankali game da muhimmancin tuntubar juna tsakanin wakilan kungiyar ta Afrika mai hedkwata a Addis Ababa.

Babbar sakatariyar hukumar ECA, Vera Songwe, ta ce matsalolin ibtila'in da ake yawan fuskanta sun isa zama shaida dake tabbatar da wajibcin daukar matakan gaggawa don shawo kan matsalolin sauyin yanayi a halin yanzu.

Songwe ta ce, yanayin da ake ciki ya sa ala tilas hukumar ECA ta himmatu wajen bada gudunmowa a kokarin da ake na rage dumamar yanayin duniya da kasa da maki 1.5 a matakin Celsius, da kuma rage tasirin illolin dake tattare da matsalar sauyin yanayi.

A cewar jami'ar ta ECA, za su cigaba da zurfafa yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa domin lalibo hanyoyin bunkasa karfin da kasashen Afrika ke da shi da tabbatar da samun dawwamamman cigaban nahiyar, da kuma rage girman tasirin illolin sauyin yanayi a nahiyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China