2019-12-10 14:16:50 cri |
Mr. Li ya ce Sin na fatan aiki tare da Sao Tome da Principe, kan manyan batutuwa da suka shafi kasashen biyu, tare da daukar matakan kare alakar kasar da kasar Sin, wadda take daya tak a duniya.
A nasa bangare Mr. Neves ya ce Sao Tome da Principe za ta nace ga akidar kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma fatan ci gaba da hadin gwiwa a fannonin makamashi, da raya kayayyakin more rayuwa, da kiwon kifi, da fannin lafiya da al'adu.
Kasashen biyu dai sun mayar da dangantakar diflomasiyyar su ne a shekarar 2016, matakin da ya bude sabon babi na kawance tsakanin sassan biyu. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China