Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi kira ga kasashen Afirka da su mai da hankali ga yaki da cin hanci domin dakile munanan laifuka
2019-12-10 10:56:20        cri
Mataimakin babban daraktan wata cibiya dake rajin kare muhalli da tattalin arziki a Afirka Leo Atakpu, ya shawarci shugabannin kasashen Afirka da su mai da hankali ga aiwatar da matakan yaki da cin hanci da rashawa, a matsayin hanyar dakile yaduwar munanan laifuka a nahiyar.

Leo Atakpu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na shiyya da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce yawa-yawan al'ummar nahiyar ba su ma fahimci mene ne ma'anar cin hanci ba, duba da yadda masu aikata shi ke zuba jari a sassa daban daban, suna samar musu da guraben ayyukan yi. Don haka a cewar sa, akwai bukatar fadakar da al'ummar nahiyar hanyoyin kandagarkin ayyukan cin hanci, da mummunan tasirin da yake yi ga tattalin arziki da ma rayukan su.

Atakpu ya kara da cewa, furta manufar yaki da cin hanci kadai ba zai wadatar ba, har sai an hada da aiki tukuru, ganin yadda da yawa daga al'ummar nahiyar ke da karancin fahimta a kan hakan.

Taron wanda aka bude a jiya Litinin, ya samu halartar kungiyoyi masu zaman kan su, wadanda suka zo daga sassan nahiyar da dama. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China