Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin ciyar da dalibai a Benin da kasar Sin ta tallafa ya haifar da sakamako mai kyau
2019-10-15 19:09:33        cri
Karamin ministan raya kasa da tsare-tsare na kasar Benin Abdoulaye Bio-Tchane, ya bayyana cewa, kasar Sin babbar abokiyar huldar shirin kasarsa ce, a fannin ciyar da dalibai da nufin kara sanya yara a makaranta a kasar dake yammacin Afirka,

Ministan ya bayyana hakan ne cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a farkon wannan wata a Cotonou, babbarn birnin kasar. Yana mai cewa, kasar ta samu kyawawan sakamako daga wannan shirin tare da taimakon kasar Sin.

Ya ce, gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen aiwatar da shirin ciyar da daliban, ta hanyar ba da taimakon kusan tan 3,800 na shinkafa da darajarsu ta kai kusan Yuan miliyan 30, kwatankacin Dakar Amurka miliyan 4.2, ya taimakawa gwamnatin Benin cimma kyawawan sakamako a karkashin wannan shiri. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China