Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin tsaron Afrika da masu ruwa da tsaki za su yi taro game da harkar tsaron nahiyar
2019-12-18 11:54:33        cri

Jiya ranar 17 ga wata, Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar cewa, ministocin tsaron kasashen Afrika, da manyan hafsoshin tsaro, da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro za su gudanar babban taro cikin wannan mako domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiyar nahiyar.

Kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta bayyana cewa, taron da za'a gudanar wani bangare ne na taron kwamitin kwararru dake kula da al'amurran tsaro da zaman lafiya wato STCDSS, wanda za'a gudanar a ranar 19 ga watan Disamba.

Ana saran babban taron nahiyar zai mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro da nufin yin nazari game da samar da ingantattun manufofin tsaron nahiyar, ciki har da batun inganta rundunar tsaro ta ko-ta-kwana ta Afrika wato (ASF), da kara kuzarin tura dakarun tsaron cikin gaggawa.

A cewar kungiyar ta AU, ana sa ran mahalarta taron za su tattauna game da yadda rundunar ASF ta gudanar da aiki yadda ya kamata, da kwarewar tura su bakin daga a kan lokaci da AU da kungiyoyin dunkulewar tattalin arziki gu daya na shiyya shiyya ke da ita, da ma matakan riga kafin tashe tashen hankula a nahiyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China