Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin kasar Sin a Jamhuriyar Benin, zai rage gibin dake akwai na cin gajiyar fasahohin zamani
2019-09-25 09:59:54        cri
Gwamnatin kasar Sin, ta bada da kayayyakin samar da shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan Adam kyauta, ga kauyuka 200 na kasar Benin, da zummar rage gibin dake akwai na cin gajiyar fasahohin zamani.

Rahoton gidan talabijin na kasar ya ruwaito cewa, gudunmuwar wani bangare ne na aiwatar da shirin samar da shirye shiryen talabijin ta tauraraon dan Adam ga kauyukan Afrika 10,000, domin cike gibin samun fasahohin zamani a kauyukan nahiyar.

A cewar Richard Owaton, shugaban kauyen Vakon na yankin Ouémé, gudunmuwar za ta amfanawa kauyen, la'akari da yadda mutane za su samu abun kallo da damar tsokaci kan rahotannin da ake watsawa a tashoshin tauraron dan Adam.

Shirin na daga cikin muhimman shirye-shirye 10 na hadin gwiwa dake da nufin karfafa zumunci tsakanin Sin da Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China