Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Masar ya ce dandalin Aswan zai taimaka wajen warware kalubalolin Afrika
2019-12-13 10:31:10        cri

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana cewa, taron dandalin Aswan mai samun dawwamamman zaman lafiya, da tsaro, da cigaba, zai kasance mafita ga nahiyar Afrika wajen tinkarar manyan kalubalolin da take fuskanta wajen neman cigaba, da sake raya kasa, da tabbatar da zaman lafiya.

Da yake gabatar da jawabin rufe taron dandalin na wuni biyu wanda aka gudanar a birnin Aswan, na kasar Masar, al-Sisi ya ce, an tattauna muhimman al'amurran da suka shafi makomar nahiyar Afrika a taron.

Ya ce, taron muhawarar, ya samu halartar shugabannin kasashen Chadi, Nijer, Senegal, Najeriya, da wakilan manyan hukumomin kasa da kasa, an gudanar da muhimman tattaunawa da nufin zakulo manyan kalubalolin dake fuskantar nahiyar tare da nazari kan matakan da ya dace a dauka wajen shawo kan matsalolin.

Shugaban na Masar ya ce, ya yi amanna kasashen Afrika a shirye suke su dauki dukkan matakan siyasa domin kawo karshen kalubaloli daban daban dake da nasaba da tsaro da samar da dawwamman cigaba.

Al-Sisi ya ce, mahalarta taron sun yi cikakken bayani da tsokaci game manyan kalubalolin dake damun Afrika, da abubuwan da suka haddasa matsalolin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China