Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasashen Afirka sun yi kira da a dukufa wajen yaki da taaddanci
2019-12-13 11:24:06        cri

A taron dandalin tattaunawar neman dauwamammen ci gaba da zaman lafiya da aka kammala a jiya Alhamis a birnin Aswan na kasar Masar, shugabannin kasashen Afirka da dama sun yi kira ga sauran kasashen duniya su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka.

A wajen taron mai taken "Afirkar da muke so, Afirka mai samun dauwamammen zaman lafiya, da tsaro, da ci gaba", shugabanni da dama sun tattauna game da kalubaloli da illolin da ta'addanci ya haifarwa kasashen Afirka ta bangaren neman ci gaba, a sa'i daya kuma sun ce, tsoma bakin da wasu kasashen suka yi a harkokin cikin gidan kasashen Afirka yana kawo koma-baya ga kasashen Afirka kan shirin yaki da ta'addanci.

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Chadi Idriss Deby sun bayyana cewa, batun sake gina kasa bayan rikice-rikice yana da muhimmanci ga kasashen Afirka, ya kamata sauran kasashe su daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Afirka, ta yadda wadannan kasashe za su samu damar farfadowar kasashensu.

A yayin taron, wakiliyar musamman ta gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin kasashen Afirka Xu Jinghu ta bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka wajen warware matsalolin da suka shafe su da kansu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China