Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a cimma ra'ayi daya wajen yaki da ta'addanci a Gabas ta Tsakiya
2019-10-29 15:33:32        cri
Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da cewa, shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi ya kashe kansa cikin wani harin da sojojin kasar Amurka suka kaddamar. A halin yanzu, akwai muhimman ayyukan dake gabanmu ta fuskar yaki da ta'addanci a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma babban kalubalen dake gabanmu shi ne, wasu kasashen yammacin duniya suna nuna bambanci kan wannan aiki, suna mayar da aikin yaki da ta'addanci a matsayin aikin neman moriya, lamarin da ya haddasa illa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci.

Ya kamata a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa wajen yaki da ta'addanci, domin rage karfin kungiyoyin 'yan ta'adda. Kuma za a iya cimma wannan buri ne ta hanyar hana samar musu da kudade da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma da dai sauransu, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da tsarin al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China