Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin musamman na MDD ya bukaci daukar matakan dakile yaduwar barazanar ta'addanci a sassan Afirka
2019-07-25 10:42:37        cri
Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a yammacin Afirka da yankin Sahel Mohamed Ibn Chambas, ya bukaci kasashen duniya da su dauki karin matakan dakile yaduwar barazanar ta'addanci a wadannan yankuna.

Ibn Chambas ya yi wannan kira ne a jiya Laraba, yayin wani taron tattaunawa na kwamitin tsaron MDD, game da halin da ake ciki a yankin yammacin Afirka da Sahel, yana mai cewa daukacin al'ummun yankin Sahel na cikin wani hali na zaman dar dar. Hakan kuwa a cewar sa, na da nasaba ne da yawaitar tashe tashen hankula da ke haifar da bukatun jin kai masu tarin yawa, al'amarin da ya jefa al'ummun kasashen Burkina Faso, da Najeriya, da Mali su kimanin miliyan 5.1 cikin bukatar agajin jin kai.

Game da batun yanayin da ake ciki a yankin tafkin Chadi kuwa, jami'in ya ce hare haren mayakan Boko Haram, na ci gaba da tada hankula, da gurgunta yanayin zaman lafiya a yankin.

Duba da yanayin da ake ciki a yankin na karuwar ayyukan ta'addanci masu da alaka da sauran muggan laifuka, da fadace fadace masu nasaba da kabilanci a yankin, kungiyar ECOWAS ta shirya gudanar da taro, game da yaki da ta'adanci a watan Satumba dake tafe a birnin Ouagadougou.

Ibn Chambas ya ce ana fatan taron zai samar da dama ta tattaunawa, game da dabatun tsaro da ya kamata a aiwatar a sassan yammacin Afirka da yankin Sahel, a kuma zakulo hanyoyin karfafa tsaron a daukacin yankunan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China