Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
António Guterres: Afrika ta zama bakin daga a fannin dakile ta'addanci
2019-07-11 13:37:27        cri

An kira taron manyan jami'ai game da matakan dakile ta'addanci, da kandagarkin tsattsauran ra'ayi a Afrika a jiya Laraba a birnin Nairobi, fadar mulkin Kenya. Yayin taron, babban magatakardan MDD António Guterres ya bayyana cewa, a halin yanzu, Afrika ta zama bakin daga a fannin dakile ta'addanci a duniya.

A cewarsa, hukumar raya kasa da kasa ta MDD wato UNDP, ta fidda wani rahoton bincikenta, wanda ke cewa rashin samun ilmi, da fama da talauci, su ne muhimman dalilai da suka haifar da yaduwar tsatsauran ra'ayi a Afrika, kuma ana fatan taron zai kara tattaunawa kan wasu batutuwa, ciki hadda matakan kandagarkin ta da hankali, da shimfida zaman lafiya, da samun bunkasuwa mai dorewa da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, António Guterres ya nuna cewa, yawan al'ummu mazauna nahiyar Afrika na kasa da shekaru 15 na haihuwa, hakan ya sa, abu mafi muhimmanci shi ne yin amfani da karfin matasa, don tinkarar ta'addanci, da kafa al'umma mai zaman lafiya da adalci, da yin hakuri da juna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China