Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 810,000 ne suka amfana daga tallafin shari'a da asusun tallafawa al;'umma na kasar Sin ya samar
2019-11-12 10:44:41        cri
Gidauniyar ba da tallafin shari'a ta kasar Sin, ta ce ya zuwa watan Oktoba, sama da mutane 810,000 ne suka amfana da tallafin shari'a da asusun tallafawa al'umma na kasar Sin ya samar.

Domin rage yawan shari'o'in dake neman tallafi da fadada ayyukan bada tallafin shari'a, aka kaddamar da aikin taimakawa shari'o'i daga asusun tallafawa al'umma na kasar, a shekarar 2009, wanda ya mayar da hankali ga shari'o'in da suka shafi wadanda ke cikin matsi kamar ma'aikatan da suka yi kaura da masu bukata ta musamman da tsoffi da kuma yara.

Tuni aikin ya lakume yuan miliyan 910, kwatankwacin dala miliyan 129.8, inda kudin da ake kashewa a kowacce shekara ya yi ta karuwa, daga yuan miliyan 50 a shekarar 2009, zuwa yuan miliyan 130 a bara.

Cikin shekaru 10 da kaddamar da aikin, an taimakawa shari'o'i sama da 530,000 na mutanen da ke cikin matsi da kuma samowa ko dawo da kudinsu na ruwa da ya kai yuan biliyan 31.2. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China