Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a kara hadin kai don magance ta'addanci
2019-08-28 13:52:07        cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya bayyana a jiya Talata cewa, kamata ya yi mambobin MDD su yi hattara kan barazanar da ta'addanci ke kawowa duk duniya, ban da wannan kuma, al'ummar duniya ta maida hankali kan ra'ayin raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya da kara hadin kai don tinkarar barazanar ta'addanci.

A gun taron kwamitin sulhu na tattauna barazanar da ayyukan ta'addanci ke kawowa zaman lafiya da tsaron duniya da aka yi a wannan rana, Wu Haitao ya bayyana cewa, ya kamata a yi amfani da karfin MDD da kwamitin sulhun wajen yaki da ta'addanci bisa ka'idar tsarin mulkin MDD. Ya ce, kamata ya yi a dauki ma'auni iri daya wajen gudanar da aikin yaki da duk wani matakin ta'addanci, da kuma mutunta ikon mulkin kasa na kasashen dake yaki da ta'addanci da kuma nauyin dake wuyan kasashe mambobin MDD dake yaki da ta'addanci. Sannan kuma da daukar dukkanin matakai daban-daban da suka dace don kawar da ta'addanci daga tushe. Wu ya kara cewa, ya kamata kasashen duniya su magance matsalolin shiyya-shiyya dake jawo hankalin duniya a siyasance da warware rikici cikin lumana, da taimakawa mambobi kasashe wajen kawar da talauci da samun bunkasuwa mai dorewa, da karfafa gwiwar fahimtar juna tsakanin al'adu da addinai mabambanta.

Ya kuma jaddada cewa, Sin na fatan kara hadin kai da kasashen duniya don tinkarar barazanar ta'addanci da kiyaye zaman lafiya da karko a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China