Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun hallaka mutane 4 a jihar Katsina ta Najeriya
2019-08-20 09:04:56        cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce, wasu 'yan bindiga sun hallaka mutane hudu, sun kuma yi awon gaba da wasu shanu a kalla 4 a ranar Lahadi, a kauyen Tsayau dake karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anaz Gezawa, ya ce tuni jami'an rundunar suka shiga binciken lamarin, tare da farautar maharan.

Harin dai ya auku ne kwana guda, bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya umarci dakarun sojojin kasar da kada su ragawa dukkanin wasu 'yan bindiga dake addabar al'ummar jihar ta Katsina.

Shugaban ya kuma umarci dakarun Najeriya da su kara azama, wajen aiwatar da matakan wanzar da zaman lafiya a dukkanin sassan kasar, musamman ma jihohin dake fama da tashe tashen hankula masu nasaba da ayyukan 'yan bindiga. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China