Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 63 sun mutu a harin kunar bakin wake a dakin taron bikin aure a Kabul
2019-08-18 16:10:22        cri

A kalla mutane 63 ne aka tabbatar da mutuwarsu kana wasu mutane fiye da 180 sun samu raunuka a daren ranar Asabar, a sakamakon harin kunar bakin wake a wani babban dakin taro dake yammacin birnin Kabul, yayin da ake tsaka da gudanar da bikin aure, 'yan sandan kasar Afghanistan sun tabbatar da faruwar lamarin.

Fashewar ta faru ne a cikin dakin taro na Shahr-e-Dubai a yayin da ake bikin aure da misalin karfe 10:40 na daren Asabar, daidai lokacin da dakin taron ya cika makil da baki dake halartar bikin wasu ma'aurata 'yan kasar Afghanistan.

Sanarwar tace, daga cikin wadanda suka mutu akwai mata da kananan yara da dama.

Ana tsammanin adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa kasancewar wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka suna cikin mawuyacin hali.

Kawo yanzu, babu wata kungiya ko wani mutum da ya yi ikirarin daukar alhakin harin.

Babban birnin kasar Afghan wanda ke da yawan al'umma kusan miliyan 5 ya sha fama da hare haren ta'addanci masu yawa a 'yan shekarun da suka gabata.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China