Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei ya yi kira da a tinkari kalubalen tsaro ta fuskar fasahar zamani bisa sanin ya kamata
2019-05-25 16:24:11        cri

Hu Houkun, mataimakin shugaban kamfanin Huawei ya bayyana cewa, ya kamata a tinkari kalubalen tsaro ta fuskar fasahar zamani bisa sanin ya kamata kuma ta hanyar hadin gwiwa.

Mista Hu ya fadi haka ne a yayin wani taro da aka gudanar dangane da batun tsaron kafar Intanet da aka yi a birnin Potsdam na kasar Jamus daga ranar 23 zuwa 24 ga wata. Inda ya kuma nuna cewa, saurin bunkasar fasahar zamani ya kawo sabbin kalubale da dama ta fuskar tsaro. Ya ce babu wani mutum ko wata kasa da za ta iya tinkarar wadannan kalubaloli ita kadai. Ya kara da cewa, yana fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki za su kimanta barazanar bisa sanin ya kamata da kuma hakikanin abubuwa, a kokarin daidaita kalubalen tare. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China