Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: ya zama tilas a nuna sahihanci domin yin tattaunawa yadda ya kamata
2019-05-23 19:53:25        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Alhamis a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta koma kan teburin tattaunawa kamar yadda ta fada. Kasar Sin na son yin tattaunawa da ita, amma ya zama tilas a nuna sahihanci, domin tattaunawar yadda ya kamata.

A 'yan kwanakin baya, rahotanni sun nuna cewa, Amurka ta sanya takunkumi kan wasu kamfanonin kimiyya da fasahar zamani na kasar Sin kamar Huawei, da DJ-Innovations, da HIKVISION, wanda ake ganin cewa, mataki ne da Amurka ta dauka domin kara matsa wa kasar Sin lamba. A sa'i daya kuma, ministan kudin Amurka Steven Mnuchin, ya ce Amurka na son ci gaba da tattaunawa da kasar Sin, tana kuma fatan kasashen 2, za su koma kan teburin tattaunawa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China