Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Amurka: tattaunawa da tuntubar juna cikin adalci, ita ce hanya ce daya tak ta kawar da sabani tsakanin Sin da Amurka
2019-05-25 16:22:22        cri

Cui Tiankai, jakadan kasar Sin a Amurka ya bayyana jiya Jumma'a cewa, tattaunawa da tuntubar juna cikin adalci, ita ce hanya daya tak ta kawar da sabani tsakanin Sin da Amurka.

Jakada Cui ya fadi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin da wakilan shirin Bloomberg Daybreak: Americas na gidan talibijin na Bloomberg TV na Amurka suka yi masa a wannan rana, dangane da batun huldar ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka.

Yayin da wakilan shirin sun tabo batun rashin tabbas kan tattaunawar da ke tsakanin kasashen 2 kan tattalin arziki da ciniki, jakadan Sin ya ce, dalilin da ya sa aka samu rashin tabbas dangane da tattaunawar shi ne, sau da dama, Amurka ta sha sauya matsayinta, sabanin kasar Sin da ba ta taba sauya matsayarta ba. Ya ce zuwa yanzu, kasar Sin ta gaskata cewa, tattaunawa da tuntubar juna cikin adalci, ita ce hanya mafi dacewa ta kawar da sabani tsakaninta da Amurka, kuma tana nan tana himmantuwa kan lamarin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China