Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Matakin da Amurka ta dauka kan Huawei babakere ne
2019-05-23 11:31:24        cri

Jiya ne mamban majalisar gudanarwar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Mista Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje na kungiyar SCO da aka yi a Bishkek, inda ya shedawa manema labarai cewa, yadda Amurka ta matsa wa kamfanin Huawei mai zaman kansa lamba, tamkar mataki ne na yin babakere.

Mista Wang ya ce, wasu Amurkawa ba su son ganin bunkasuwar kasar Sin ba, kuma suna kokarin kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Alal misali, yadda Amurka ta dauki mataki kan kamfanin Huawei mai zaman kansa na kasar ta Sin ba gaira ba dalili, ko shakka babu wannan mataki wani kokari ne na yin babakere. Duk wanda ke samun goyon bayan al'umma, tabas zai samu taimako daga gare su, yayin da wanda ba ya samun irin wannan goyon bayan, ba shakka babu wanda zai taimaka masa. Matakin da Amurka ke dauka na nuna girman kai ba zai samu amincewar al'ummar duniya ba ko kadan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China