Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shehun malami a jami'ar Yale: dole ne Amurka ta yi koyi da tarihi, a kokarin sake maimaita kuskuren baya
2019-05-20 20:08:59        cri

Shehun malami a jami'ar Yale ta kasar Amurka Stephen Roach, ya bayyana a kwanan baya cewa, yadda gwamnatin Donald Trump ta kara dora kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin take sayarwa a Amurka, ya kusa daidai da yadda Amurka ta aiwatar da manufar ba da kariya kan ciniki a shekarun 1930.

Masanin a fannin ilmin tattalin arziki ya yi kira ga gwamnatin Trump, da ta dakatar da ba da kariya kan ciniki, ta yi koyi da tarihi a kokarin sake maimaita kuskuren baya.

Yayin da yake zantawa da wakilin gidan talibijin na Bloomberg, wanda ya shahara wajen watsa labaru game da hada-hadar kudi da tattalin arziki, Stephen Roach ya ce, abubuwan da suka faru a tarihi sun yi kashedin cewa, Amurka tana dab da sake maimaita kuskuren baya, wanda hakan ya faru saboda shugaban Amurka a wancan lokaci bai saurari shawarar kwararru ba.

Yawancin masana masu ilmin tattalin arziki suna ganin cewa, yadda Amurka ta aiwatar da manufar ba da kariya kan ciniki a shekarun 1930, shi ne babban dalilin da ya tsananta tabarbarewar tattalin arzikin Amurka a shekarun 1930. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China