Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kungiyoyin masu sana'o'i na Amurka sun bukaci gwamnatin kasar da ta gyara kuskurenta
2019-05-24 20:25:51        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana yau Jumma'a cewa, yanzu haka kasashen Sin da Amurka sun gaza hada kai domin samun moriyar juna, kuma sun gaza kawar da sabani ta hanyar tattaunawa cikin lumana kamar yadda suka yi a baya. Kaza lika kasashen biyu sun gaza ci gaba da kiyaye moriyarsu ta bai daya, amma kuma wannan ba kuskure ne na kasar Sin ba.

Kalaman na Lu Kang sun biyo bayan bukatun wasu kungiyoyin masu sana'o'i na kasar Amurka, wanda suka bukaci gwamnatin kasarsu da ta gyara kuskurenta,

Rahotanni sun ce, jiya Alhamis shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da kara samar wa manoman kasar tallafin kudi na dalar Amurka biliyan 16. Amma wani dan majalisar dattawan kasar ya aike da wasika zuwa ga ministan aikin gona na kasar, yana mai cewa, kudin diyyar da ma'aikatar gonan kasar ta biya wa manoman, bai wuce kashi 1 cikin kashi 3 kacal, na jimillar asarar da manoma suka yi a bara ba.

Yanzu haka yawan kudin shiga da kasar Amurka ta samu a fuskar aikin gona ya ragu da kaso 50% idan an kwatanta da na shekarar 2013. Hakan na nuna cewa, manoma da yawa suna dab da shiga fatarar kudi. Don haka ya bukaci shugaba Donald Trump, ya kawo karshen takaddamar cinikayya a tsakanin Amurka da Sin nan da nan. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China