Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: dukkan kamfanoni ba za su bi umurnin wata kasa bisa son kai ba
2019-05-23 20:10:11        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kowa ya fahimci yadda kamfanin Huawei yake bude kofa, da hada kai da takwarorinsa na ketare, kuma yana da karfin zuciya. Hakan na nuna cewa duk wanda yake da budaddiyar zuciya, zai kai ga cimma babbar manufa. Lu Kang ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a nan Beijing, yana mai cewa, kamfanoni na ko wace kasa ba za su cutar da moriyar kansu ba, ta hanyar bin umurnin da wata kasa ta bayar bisa son kai kawai.

A kwanan baya, akwai wasu labarun da ke cewa, wasu kamfanonin ketare, sun dakatar da samar wa kamfanin Huawei kayayyaki, sakamakon takunkumin da gwamnatin kasar Amurka take sanyawa kamfanin na Huawei. Amma kamfanin Infineo na kasar Jamus, da kamfanin Panasonic na kasar Japan, sun ba da sanarwa a kwanan baya cewa, suna ci gaba da samar wa kamfanin Huawei kayayyaki. Haka kuma kamfanin EE na kasar Birtaniya ya sake nanata cewa, zai ci gaba da yin amfani da injunan da kamfanin Huawei ya kera, wajen gudanar da ayyukan fasahar 5G a kasar.

Kakakin kamfanin Huawei ya yi bayani da cewa, wasu abokan hadin gwiwa na kasa da kasa sun fuskanci matsin lamba daga Amurka ta fuskar siyasa. Amma kamfanin Huawei na da karfin zuciya kan jure wahala, da samun ci gaba mai dorewa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China