Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bambancin tunani ba ya hana yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, in ji jami'in kasar Sin
2019-05-24 20:20:00        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana yau Jumma'a cewa, idan an yi la'akari da abun da ke faruwa a duniyar nan, za a fahimci cewa, bambancin tunani ba ya hana yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ta fuskar tattalin arziki, ciniki, kimiyya da fasaha. Kana kuma tunani kusan iri daya ba zai hana kasar Amurka ta kulla makarkashiya ga kawayen nata ba.

Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce kamfanin Huawei yana da alaka da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma gwamnatin kasar ta Sin, lamarin da zai kawo wa Amurka babbar barazana idan ta yi amfani da injunan kamfanin Huawei. Yayin da ya amsa tambayar manema labaru dangane da abubuwan shaida da ke tabbatar da cewa, kamfanin Huawei yana iya leken asiri ta hanyar na'urorin sa. Jami'in Amurka ya ce, idan kamfanin ya mika wa JKS bayanan, za su iya zama barazana. Kuma wai Amurka tana taimakawa sauran kasashen duniya da kamfanoni su fahimci hakan. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China