in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakan kandagarkin cutar mura da ke yaduwa tsakanin mutane
2020-03-24 13:15:18 cri

A ko wace shekara, daga watan Nuwamba zuwa watan Maris na shekara mai zuwa, kasashen da ke yankin arewacin duniyarmu kan fuskanci babbar barazanar yaduwar annobar cutar mura wadda ke yaduwa tsakanin mutane. Don haka yau mun gayyaci Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, don ta yi mana karin bayani kan matakan da suka dace mu dauka wajen yin kandagarkin cutar mura.

Annobar cutar mura, wani nau'in cuta ce da ke yaduwa tsakanin mutane sakamakon wata kwayar cuta dake yaduwa a hanyoyin numfashi. Wadanda suka kamu da cutar kan yi zazzabi, ciwon kai, tari da ciwon jijiya da gabbai. A lokacin da aka yi fama da cutar mura daga shekarar 2019 zuwa 2020, ya zuwa yanzu a kalla mutane miliyan 29 ne suka kamu da cutar a kasar Amurka, inda kuma wasu dubu 16 suka rasa rayukansu sakamakon cututtukan da suke da nasaba da cutar mura. Hakika akwai matakai guda 5 masu sauki da za a iya dauka domin yin kandagarkin annobar yadda ya kamata, a ciki akwai yin allurar rigakafin cutar ta fi dacewa, kuma ya fi muhimmanci.

Madam Zhang Chuji ta yi mana karin bayani da cewa, yin allurar rigakafin cutar mura a ko wace shekara, hanya ce mafi dacewa wajen kare kanmu daga kamuwa da cutar da kuma sauran munanan cututtukan da suka biyo bayan kamuwa da ita.

Yin allurar rigakafin yana da matukar muhimmanci ga masu juna biyu, kananan yara wadanda shekarunsu suka wuce watanni 6 amma ba su kai 6 a duniya ba, tsofaffi, maras lafiya dake doguwar jinya da ma'aikatan kiwon lafiya, kamar su likitoci da nas-nas.

Wasu suna nuna damuwar cewa, ko yin allurar rigakafin cutar mura za ta iya yin illa ga lafiyar mutane. Dangane da wannan, madam Zhang Chuji ta jaddada mana cewa, yin allurar rigakafin cutar mura ba zai sa mutane su kamu da mura ba. Yawancin mutane su kan ji ciwo ko kuma yin zazzabi bayan da aka yi musu allurar. Irin Wannan ciwo ko zazzabi kan dauki kwanaki 2 ne kawai. Don haka, ba abu ne na damuwa ba ko kadan.

To, ban da yin allura rigakafin annobar cutar ta mura ta Flu, akwai sauran matakai guda 4 masu saukin aiwatarwa wajen kare kanmu daga kamuwa da annobar. Madam Zhang Chuji ta ci gaba da cewa, wanke hannunmu a kai a kai, magance taba idanunmu, hancinmu da bakinmu, nisantar masu fama da cutar ta mura, da hutawa a gida idan ba a ji dadin jiki su ma suna da amfani sosai wajen kare kanmu daga kamuwa da cutar ta mura.

Likitar ta yi bayani da cewa, tabbatar da tsabtar hannayenmu, hanya ce mafi sauki wajen kare kanmu da iyalinmu daga kamuwa da cututtukan da ke yaduwa tsakanin mutane. Kwayoyin cutar mura, sun fu saukin shiga cikin jikinmu ta idanunmu, hancinmu da bakinmu. Ana iya dakile yaduwar annobar ta hanyar magance taba abubuwa. Kwayoyin cutar Flu suna yaduwa tsakanin mutane, musamman ma wajen cunkuson mutane, alal misali, a cikin ababen hawa, makarantu da sauran wuraren da a kan samu taruwar mutane. Haka zalika, idan mutum ya kamu da cutar mura, kamata ya yi ya huta a gida, kada ya je aiki ko makaranta. Ya fi kyau ya kebe kansa daga iyalinsa da sauran mutane kan lokaci, hakan zai taimaka wajen dakile yaduwar annobar da kuma ceton mutane.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China