lafiya1811.m4a
|
Kwanan baya, hukumar ilmin jinyar kananan yara ta kasar Amurka, ta kaddamar da littafin ba da shawara, inda ta yi nuni da cewa, illar da ruwan 'ya'yan itatuwa ke yi wa lafiyar kananan yara da shekarunsu ba su wuce 1 da haihuwa ba, ta fi amfanin da suke yi ga lafiyarsu yawa. Don haka bai kamata ba iyaye su shayar jarirai ruwan 'ya'yan itatuwa.
Kafin hakan, hukumar ilmin jinyar kananan yara ta Amurka, ta shawarci iyaye da kada su shayar da jariran da ba su kai watanni 6 a duniya ba ruwan 'ya'yan itatuwa. Amma sakamakon karuwar shaidu da suka nuna cewa, kila shan ruwan 'ya'yan itatuwa zai haifarwa yaran ciwon hakora da matsalar kiba, ya sa hukumar ta tsai da kudurin tsawaita lokacin da yaran suka shafe a duniya daga watanni 6 zuwa shekara guda.
Wani marubucin wannan littafi na ba da shawara ya bayyana cewa, watakila iyaye suna ganin cewa, ruwan 'ya'yan itatuwa na da amfani ga lafiya. Amma kuma yana kunshe da karin sukari da Calorie, kuma bai dace a sha ruwan 'ya'yan itatuwa a maimakon cin danyun 'ya'yan itatuwan ba. Kana kuma, idan kananan yara sun dan yi girma, suna iya shan ruwan 'ya'yan itatuwa kadan. Amma babu butakar shayar da kananan yara da shekarunsu suka wuce 1 a duniya ruwan 'ya'yan itatuwa.
Bisa tanade-tanaden da ke cikin littafin ba da shawarar, an ce, bai kamata ba a shayar da kananan yara da shekarunsu suka wuce 1 amma ba su kai 3 a duniya ba ruwan 'ya'yan itatuwa da yawansa ya wuce milliliter 118 a ko wace rana, yayin aka ce kada yara da shekarunsu suka wuce 4 amma ba su kai 6 a duniya ba su sha ruwan 'ya'yan itatuwa da yawansa ya wuce milliliter 177 a ko wace rana. Sa'an nan kada yara da shekarunsu suka wuce 7 amma ba su kai 18 a duniya ba su sha ruwan 'ya'yan itatuwa da yawansa ya wuce milliliter 237 a ko wace rana. Har ila yau an shawarci iyaye da kada su shayar da yaransu ruwan 'ya'yan itatuwa na cikin kwalaba, da kuma abun zuka kafin yaransu su yi barci.
Haka zalika, da kakkausar murya wannan littafin ba da shawara ya soki barin yara su sha abun sha mai kunshe da ruwan 'ya'yan itatuwa wanda ba a kashe kwayoyin cutar sa ta hanyar tsananin zafi ba. Sa'an nan kuma, kada yaran da suke shan wasu magungunan musamman su sha ruwan garehul, saboda ruwan ya kan raunana amfanin magungunan da suke sha. Bayan haka kuma, idan yara suna fama da tauyewar ruwa da ke jikinsu da kuma zawayi, to bai dace ba su sha ruwan 'ya'yan itatuwa.
Hukumar ilmin jinyar kananan yara ta Amurka ta yi nuni da cewa, babu isassun sinadaran dake taimakawa narkas da abinci a jikin mutum a cikin ruwan 'ya'yan itatuwa. Don haka ya kamata iyaye su kara karfafa gwiwar yaransu su ci danyun 'ya'yan itatuwa. (Tasallah Yuan)