in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsoffi: kara motsa jiki yana iya kare su daga fadawu
2018-02-23 14:12:18 cri

Sakamakon wani sabon nazari ya shaida cewa, kara motsa jiki yana iya kare tsoffafi daga jin rauni sakamakon fadawu a kasa.

Kwanan baya, masu nazari daga asibitin St. Michael na kasar Canada sun wallafa wani rahoton nazarinsu a cikin mujallar hukumar ilmin likitanci ta kasar Amurka, inda suka nuna cewa, sun tantance nazarce-nazarce 54 masu ruwa da tsaki da aka gudanar da ka, wadanda suka shafi tsoffafi kusan dubu 42, wadanda shekarunsu suka wuce 65 da haihuwa, da kuma hanyoyi guda 39 na yin rigakafin fadawu a kasa.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, yin wasan Tai Chi da sauran hanyoyin motsa jiki suna iya taimaka wa tsoffi wajen rage barazanar jikkata sakamakon fadawu a kasa da kashi 12 cikin dari. Idan aka yi bincike kan idanunsu tare da yi musu jinya, hakan zai iya rage irin wannan barazana da kashi 38 cikin dari.

Ban da haka kuma, kyautata muhallin da tsoffi suke zaune da kuma shan sinadarin Calcium da muhimman sinadarai da jikin dan –Adam ke bukata, su ma suna iya taimakawa tsoffi wajen rage barazanar fadawu a kasa.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, fadawu a kasa yana kawo babbar illa ga lafiyar tsoffi. Kana kuma, yanzu yawan tsoffi na ci gaba da karuwa a duk fadin duniya, don haka, yawan tsoffin da suke faduwa a kasa zai yi ta karuwa. Yanzu haka sun lalubo hanya mafi dacewa ta rage barazanar fadawu a kasa. Motsa jiki yana da amfani sosai. Ko da yake watakila motsa jiki zai kara haifar da wasu wasu matsaloli da barazanar fadawu a kasa, amma rashin motsa jiki ya fi kawo wa tsoffi barazana.

Masu sharhi sun bayyana ra'ayinsa dangane da wannan rahoton nazari, inda suka ce, fadawu a kasa, shi ne babban dalilin da ya sa tsoffafin da shekarunsu suka wuce 65 suka ji rauni. Wannan rahoton nazari ya jaddada muhimmiyar rawa da motsa jiki yake takawa ga tsoffafi wadanda suka dade suna zaune ko kuma ba su motsa jiki ba sakamakon fama da ciwo. Har ila yau, masu sharhin sun ce, kamata ya yi likitoci su mai da hankali kan masu fama da wata lalura da ke haifar da barazanar fadawu a kasa. Amma babu wani dalilin da zai hana yawancin tsoffafi su motsa jiki yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China