in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila cin jan barkono kullum yana iya kara tsawon rai
2018-03-11 13:47:07 cri

Masu karatan shafinmu barkan ku da wannan lokaci, shin kuna ci ko sha'awar cin abu mai yaji? To. Albishirinku! Idan haka ne watakila za ku yi tsawon rai. Wani sabon nazari ya shaida mana cewa, cin jan barkono kullum yana taimakawa wajen rage mace-mace, musamman ma mutuwa sakamakon ciwon zuciya da shan inna.

Kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Vermont ta kasar Amurka ya kaddamar da sakamakon nazarinsa a kwanan baya, inda ya tantance bayanan da aka samu daga wani nazari na daban da aka gudanar dangane da lafiyar Amurkawa dubu 16 da kuma yadda suka ci abubuwa masu gina jiki, musamman ma nazari game da lafiyar wadannan Amurkawa bayan da suka ci jan barkono. A cikin wannan nazarin da aka gudanar dangane da lafiyar Amurkawa dubu 16 da kuma yadda suka ci abubuwa masu gina jiki, lokaci mai tsawo da aka dauka ya kai shekaru 23 baki daya.

Sakamakon da kwalejin ya fitar ya shaida mana cewa, a lokacin gudanar da nazarin, yawan wadanda su ka ci jan barkono da suka mutu ya kai kaso 21.6 cikin dari bisa jimillar Amurkawa dubu 16, yayin da yawan wadanda ba su ci jan barkono ba da suka mutu ya kai kashi 33.6 cikin dari. Sakamakon yin la'akari da shekarunsu na haihuwa, jinsi, yanayin zaman rayuwarsu, kamuwa da cuta ko a'a da dai sauransu, ya sa ake ganin cewa, yawan wadanda su kan ci jan barkono da suka mutu ya yi kasa idan da kwatanta da yawan wadanda ba su ci jan barkonon ba da kashi 13 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayani cewa, ko da yake mai yiwuwa ne jan barkono zai iya taimakawa wajen kara tsawon rai, amma yanzu ba a san ta wane fanni yake aiki ba tukuna. Sun kuma yi hasashen cewa, watakila dalilin da ya sa haka shi ne domin sinadarin Capsaicin da ke cikin jan barkonon yana taimakawa wajen hana yin kiba, da kuma kyautata gudanar jini cikin jijiyoyin jini a zuciya, lamarin da ya bayyana dalilin da ya sa barazanar mutuwa sakamakon ciwon zuciya da shan inna da wadanda su kan ci jan barkono kullum suke fuskanta ta yi kasa. Har ila yau kuma, sinadarin Capsaicin yana iya yakar wasu kwayoyin cuta, da kyautata kananan halittu masu rai a cikin hanji, ta yadda sinadarin zai taimakawa lafiyar mutane.

Ko shakka babu, ba dukkan mutane ba ne za su dauki lokaci mai tsawo suna ci jan barkono ba. Alal misali, kamata ya yi wadanda suke fama da matsalar narkar da abinci su yi taka tsan-tsan yayin da suke cin jan barkono. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China